Isa ga babban shafi
Duniya

Faransa na lallashin Iran kan tsagaita wuta a Syria

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian, na wata ziyara a Tehran Babban birnin Iran da nufin jaddada goyon bayan faransa kan cigaba da mutunta yarjejeniyar kera makamin nukiliyarta, tare kuma da lallashin Iran din kan sassauta rawar da take takawa a yakin kasar Syria.

A na saran Jean-Yves Le Drian zai rarrashi Iran din don ta rage rawar da ta ke takawa a yakin basasar Syria yayinda kuma zai jaddada goyon bayan Faransa kan yarjejeniyar nukiliyarta.
A na saran Jean-Yves Le Drian zai rarrashi Iran din don ta rage rawar da ta ke takawa a yakin basasar Syria yayinda kuma zai jaddada goyon bayan Faransa kan yarjejeniyar nukiliyarta. Tasnim News Agency/Handout via REUTERS
Talla

Wannan dai ita ce ziyara ta farko da wata kasa cikin kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran ke kai wa tun bayan da shugaba Trump ya sanya wa’adin ficewa daga cikin ta, idan har aka gaza cimmawa wasu sabbin sharudda.

Gabanin ziyarar ta sa ta yau ministan harkokin wajen na Faransa yayi wani tsokaci kan goyon bayan shirin Nukiliyar Iran, matakin da ya janyo masa suka daga kasashen Turai.

Kai tsaye dai le Drain zai yi wata tattaunawa ta kai tsaye da takwaransa na harkokin wajen Iran Muhammad Javad zarif, gabanin ganawar su da Ali Shamkani sakataren majalisar kolin tsaron kasar, yayinda ake saran zai rarrashi kasar don rage karsashi a rawar da take takawa a yakin Syria.

Kasashen yammaci dai sun jima suna zargin Iran da hannu a yakin Syria matakin da  Tehran din ta sha musantawa, ko da dai a yan kwanakin baya anyi fito na fito tsakanin dakarunta da na Isra’ila, abunda ke gasgata hannunta a yakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.