Isa ga babban shafi
Brazil

Wakilan Majalisar Dattijai na Brazil sun amince soja su kula da tsaro a Rio de Janeiro

Majalisar Dattijan kasar Brazil ta amince da tura soja birnin Rio de Janeiro domin tabbatar da doka da oda a garin sakamakon sukurkucewar harkan tsaro saboda rikici da dillalan miyagun kwayoyi ke yi.

Shugaban Brazil Michel Temer
Shugaban Brazil Michel Temer rfi
Talla

Duk da zargin cewa amfani da karfin soja na iya yin katsalandan da take hakkin jama’a da kundin tsarin mulki ya tanadar, wakilan majalisar Dattijan sun zartas da tura soja da gagarumin rinjaye inda wakilai 55 suka amince, wasu 13 suka ki amincewa, sai kuma wani dan majalisa daya da yaki jefa kuria.

Shugaban kasar Michel Temer tuni ya zartas da wannan doka da umarnin sojan kasar su fara aikin tabbatar da tsaro a birnin Rio de Janaeiro daga Juma’a mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.