Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Dole al'ummar Zimbabwe su yi zabe- Amurka

Amurka ta ce dole ne a bai wa al’ummar Zimbabwe damar kada kuri’a don zaben gwamnatin da suke bukata ta hanyar demokradiya bayan sojoji sun karbe ikon tafiyar da kasar.

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe
Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe REUTERS/Stringer/File Photo
Talla

Gabanin ganawarsa da Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Afrika a birnin Washigton, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ya ce, ya kamata su yi aiki tare don gaggauta maido da mulkin farar hula a Zimbabwe.

A yau ne dai shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya bayyana a bainal jama’a, in da ya halarci bikin yaye dalibai a wata jami’a da ke birnin Harare duk da cewa mulki na hannun sojojin kasar.

Amurka dai ba ta dasawa da shugaba Mugabe wanda ya shafe tsawon shekaru 37 yana jagorancin kasar tun bayan samun ‘yancinta daga turawan Birtaniya a shekarar 1980.

Karbe mulkin na zuwa ne bayan shugaba Mugabe mai shekaru 93 ya kori mataimakinsa Emmerson Mnangagwa, yayin da masharhanta ke cewa, ya yi haka ne don share wa uwargidarsa Grace Mugabe hanyar darewa kan kujerar shugabancin kasar bayan saukarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.