Isa ga babban shafi
MDD

Ko MDD za ta iya samar da sauye-sauye kuwa?

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya lashi takobin samar da sauye-sauye na ci gaba a Majalisar wadda ta fara taronta na 72 a birnin New York. Wannan na zuwa ne a yayin da shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, Majalisar ta gaza sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.

Sakatare Janar na Majalisar dinkin Duniya  António Guterres a zauren Majalisar da ke birnin New York na Amurka
Sakatare Janar na Majalisar dinkin Duniya António Guterres a zauren Majalisar da ke birnin New York na Amurka REUTERS/Lucas Jackson
Talla

Da dama daga cikin masharhanta kan siyasar duniya na ci gaba da diga ayar tambaya kan ko Majalisar Dinkin Duniya na aiki tukuru don samar da sauye-sauyen ci gaba a kasashen duniya?

Majalisar dai na shan caccaka game da yadda take tafiyar da al’amuranta da kuma yadda take nuna fifiko tsakanin manyan kasashen duniya masu karfin fada a ji da kasashe masu tasowa.

Ana dai kallon Majlisar Dinkin Duniya a matsayin wata cibiyar samar da zaman lafiya a duniya, amma ta gaza wajen sauke wannan nauyi, musamman a kasashen da ke fama da rikice-rikice maban-banta da suka hada da rikicin addini da siyasa da kuma kabilanci, baya ga matsalar ‘yan gudun hijira da ke ci gaba da kwarara zuwa kasashen Turai daga nahiyar Afrika da Asiya.

Har ila yau Majalisar na shan suka saboda yadda ta gaza samar da sauyi a tsarin tafiyar da Kwamitin Sulhu, saboda mambobin kwamitin masu kujerun din-din-din sun ki amince da haka.

Sakatare Janar, Antonio Guterres ya lashi takobin samar da sauye-sauye a Majalisar wadda ta fara gudanar da taronta na 72 a birnin New York na Amurka.

To ko daga ina zai fara tinkarar wadannan kalubale da ke gabansa?

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.