Isa ga babban shafi
Myanmar

Suu Kyi ta soke halartar taron MDD saboda rikicin Rohingya

Jagorar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi ta soke halartar taron Majalisar Dinkin Duniya da za a fara gudanarwa a makon gobe saboda rikicin 'yan kabilar Rohingya.

Jagorar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi
Jagorar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi REUTERS/Soe Zeya Tun
Talla

Mai Magana da yawunta Zaw Htay ya ce, mataimakin shugaban kasar, Henry Van Thio zai wakilce ta wajen taron na shekara-shekara.

Suu Kyi ta gamu da mummunar suka daga kasashen duniya da suka hada da masu goyon bayanta kan yadda ta kawar da kai daga kisan da sojojin kasar ke yi wa 'yan Kabilar Rohingya.

Shugaban hukumar kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya, Zeid Ra'ad al-Hussain ya bayyana kisan a matsayin yunkurin share wata al'umma daga doron-kasa.

Yau ake saran Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani taro na musamman don tattaunawa kan rikicin Myanmar.

Kimanin Musulman Rohingya dubu 400 ne suka tsere zuwa Bngladesh tun bayan barkewar rikcin a cikin watan jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.