Isa ga babban shafi
China-Amurka

China ta gargadi Amurka da Koriya ta Arewa

Kasar China ta danganta tsamin dangantaka da ke tsakanin Koriya ta Arewa da Amurka, tamkar jiragen kasa biyu da ke shirin yin taho-mu-gama, inda ta yi gargadi ga kasashen biyu su kai zuciya nesa.

China ta gargadi Amurka da Koriya ta Arewa su kai zuciya nesa bayan Koriya ta Arewar ta yi gwajin makamai masu linzami a farkon wannan makon
China ta gargadi Amurka da Koriya ta Arewa su kai zuciya nesa bayan Koriya ta Arewar ta yi gwajin makamai masu linzami a farkon wannan makon AFP
Talla

China ta bukaci Koriya ta Arewa ta dakatar da shirinta na mallakar makaman Nukiliya, tare da yin kira ga Amurka da Koriya ta Kudu su jingine atisayen da suke yi domin wanzar da zaman lafiya.

China ta yi wannan gargadin ne saboda yadda rikicin Koriya ta Arewa da Amurka da kuma Koriya ta Kudu ke yin barazana ga zaman lafiyar yankinsu.

A lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, ministan harakokin wajen China Wang Yi ya ce, Koriya ta Arewa da Amurka kamar jiragen kasa ne da shirin yin taho mu gama.

Amma Mista Wang ya bukaci bangarorin biyu su taka burki saboda zaman lafiyar yankin.

Sannan ya yi kira ga Koriya ta Arewa ta jingine shirye-shiryenta na Nukiliya da mallakar makamai masu linzami tare da yin kira kuma ga Amurka da aminiyarta Koriya ta Kudu su jingine atisayen da suke na soji wanda ke harzuka Koriya ta Arewa.

A ranar litinin dai Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamai 4 da ta ce gwaji ne na kokarin kai wa sansanonin Amurka da japan hari.

China dai na son a dawo teburin sulhu tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa musamman yadda barazanar ta kara girma bayan rantsar da Donald Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.