Isa ga babban shafi
Amurka-Koriya Ta Kudu

Amurka ta aika na'urorin garguwa a Koriya ta Kudu

Amurka ta fara aike wa da wasu manyan na’urorin garkuwa ga makamai masu linzami zuwa Koriya ta Kudu, bayan Koriya ta Arewa ta yi gwaje-gwajen makamai hudu a jiya Litinin, abin da ya saba wa dokkokin Majalisar Dinkin Duniya.

Amurka ta fara aike wa da na'urorin garkuwa ga makamai masu linzami zuwa Koriya ta Kudu bayan Koriya ta Arewa
Amurka ta fara aike wa da na'urorin garkuwa ga makamai masu linzami zuwa Koriya ta Kudu bayan Koriya ta Arewa Reuters/KCNA
Talla

Kafafen yada labaran Koriya ta Arewa sun rawaito cewa, shugaban kasar Kim Jong Un ne ya jagoranci gwajin makaman masu linzami da sojoinsa harba, kuma a yayin da sojojin Amurka ke atisayen hadin gwiwa tare da takwarorinsu na Koriya ta Kudu.

Ana ganin dai an harba makaman ne da nufin far wa sansanonin sojin na Amurka da ke Japan, abin da Washington ke kallo a matsayin tsananta barazana a gare ta.

Kwamandan runduar sojin Amurka a yankin Pacific, Admiral Harry Harris ya ce, gwaje-gwajen makaman da Koriya ta Arewa ke ci gaba da yi, sun tabbatar da muhimmancin shirinsu na hadaka da suka fara a bara, da nufin aike wa da na’urorin garkuwa ga makaman a Koriya ta Kudu.

Sai dai watakila matakin Amurkan zai iya tsananta sabani tsakanin Koriya ta Kudu da China, wadda ta ce, matakin zai yi illa ga sha’anin tsaro a yankin.

Makaman da Koriya ta Arewan ta harba sun fada cikin teku a kusa da yankin Arewa maso Yammacin Japan, lamarin da ya bakanta ran Seoul da Tokyo, kuma hakan na zuwa ne kwanaki kadan da Pyongyang ta yi alkawarin mayar da martani ga atisayen sojin da ta dauka a matsayin shirin yakar ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.