Isa ga babban shafi
Turkey-Germany

Turkiyya da Jamus na son kungiyar NATO ta hana safarar 'Yan Gudun hijira

Shugaban Gwamnatin Jamus da Shugaban kasar Turkiyya sun kammala wani tattaunawa a birnin Ankara da kira ta musamman ga kungiyar NATO domin kawo karshen safarar 'Yan Gudun hijira zuwa Turai ta teku mai hatsarin gaske.Wannan mataki na zuwa ne a wani lokaci da aka sami hasarar rayukan 'Yan Gudun hijira akalla 35 a kogin Turkiyya zuwa Girka.  

Uwargida Angela Merkel da Ahmet Davotoglu
Uwargida Angela Merkel da Ahmet Davotoglu rfi
Talla

A cewar Shugaban Gwamnatin Jamus Uwargida Angela Merkel, bayan ta tattauna da Fira Minstan Turkiyya Ahmet Davutoglu za su yi amfani da taron Ministocin Tsaro na NATO, da za'a fara jibi Laraba, su tattauna batun Syria da kuma yadda za'a taimaka domin sa ido kan bakin haure da 'Yan Gudun hijira dake saida rai abi teku zuwa Turai.

Wannan ganawa dai na zuwa ne a daidai wani lokaci da mutane 35 suka gamu da ajalinsu a kogin Aegean,  a lokacin da suke tsallakawa daga Turkiyya zura Girka, yayin da kwalekwalensu ya kife.

Majiyoyin samun labarai na cewa mutane hudu aka sami tsamosu daga kogin suna da sauran numfashi.

Hatsarin na littini, na zuwa ne bayan wanda ya auku dan tsakanin nan inda mutane sha daya  suka mutu a lokacin da kwale-kwale da suke ciki ya nutse.

Kasar Turkiyya wadda take da ‘yan gudun hijira akalla miliyan biyu da dubu dari biyar  yawanci daga kasar Syria inda ake ta yaki, ta kasance zangon farko na wadanda ke tsallakawa zuwa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.