Isa ga babban shafi
India-Afrika

India za ta yi taro da Afrika kan kasuwanci

Kasar India za ta dauki nauyin wani taro tsakaninta da shugabanin kasashen Afirka a makon gobe, a yunkurin da take yi na kutsa kai nahiyar domin bunkasa kasuwanci da zuba jari.

Firaministan India Narendra Modi
Firaministan India Narendra Modi Reuters/Rafiqur Rahman
Talla

Taron wanda shi ne irin sa na farko a karkashin jagorancin Firaministan India Narendra Modi, zai samu halartar shugabanin kasashe 40 da suka tabbatar cewa za su amsa gayyatar, cikin su har da shugaba Omar Hassan al Bashir na Sudan wanda kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ke neman sa ruwa a jallo

Kasar China dai ta mamaye tagomashin India wajen huldar kasuwanci da Afirka, inda a bara kawai ta yi cinikin dala Amurka biliyan 200 a nahiyar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.