Isa ga babban shafi
Duniya

Bincike ya nuna cewa shugabannin duniya suna amfani da dandalin Twitter

Wani bincike ya nuna cewa shugabannin kasashen duniya da dama na amfani da dandalin musayar ra’ayi, na twitter wajen yada manufofinsu da gudanar da harkokin diplomasiya a yayin da wasu daga cikinsu su ka yi watsi da wannan kafa.Binciken ya nuna cewa, 11 daga cikin shugabannin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya suna amfani da wannan dandalin na twitter, in ji Matthias Lufkens, wanda shi ne shugaban cibiyar da ta jagoranci binciken.Sai dai ya nuna rashin jin dadin sa ganin cewa shugabannin kasashen Sin, wato China, Saudi Arabia, Indonesia da Italia ba sa amfani da wannan kafar ta twitterBinciken ya kara nuna cewa, kusan kashi biyu a cikin kashi uku na shugabannin duniya, na amfani da dandalin, sai dai kadan daga cikinsu ne kan yi amfani da shi wajen tuntubar takwarorinsu.Haka kuma, shugaban tarayyar Turai, Herman Van Rompuy shi ya fi kowa amfani da dandalin na twitter inda ya kan gana da 11 daga cikin takwarorinsa.Binciken ya kuma kara nuna cewa, shugaban Amurka, Barack Obama shugabanni kasashe biyu kawai ya ke bi a danadalin na twitter, wato da firaministan Norway, Jens Stoltenberg da Firaministan kasar Rasha, Dmitry Medvedev.Haka kuma binciken ya nuna cewa, ‘Yan Siyasa na amfani da dandalin na Twitter amma sukan watsar da shi da zaran sun dare karagar mulki.Inda ya kara da cewa, shugaban kasar Faransa, Francoir Hollande da shugaban kasar Brazil Dilma Roussef na daga cikin wadanda su ka yi watsi da dandalin na twitter tun da su ka dare karagar mulki. 

Alamar shafin Twitter
Alamar shafin Twitter
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.