Isa ga babban shafi
Brazil

Sojoji dubu 43 na fafutukar kashe gobarar dajin Amazon

Sojojin Brazil sama da dubu 43 da taimakon jiragen sama ke ci gaba da kokarin kashe mahaukaciyar gobarar da ke kone dajin Amazon, mafi girma a duniya.

Wani sashin Amazon da mahaukaciyar gobarar daji ta kone.
Wani sashin Amazon da mahaukaciyar gobarar daji ta kone. REUTERS/Bruno Kelly
Talla

Yanayin na zuwa ne a dai dai lokacin da masana a Brazil suka bada tabbacin sake tashin wutar a Karin wasu sassan na dajin Amazon, da adadinsu ya kai dubu 1 da 130 a tsakanin Juma’a zuwa jiya asabar.

Zalika wata kididdiga da masanan suka fita ya nuna cewa a shekarar da muke ciki kadai an samu tashin gobarar daji a Brazil sau dubu 79 da 513, yanayi mafi muni tun bayan shekarar 2013.

Binciken masanan ya kuma ce mafi akasarin gobarar dajin na aukuwa ne a dajin na Amazon, da masana kimiyya ke yiwa lakabi da huhun duniya, la’akari da cewa yana taka rawar fitar da kashi 1 bisa 5 na iskar Oxygen dadan adam ke shaka.

Tuni dai shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasashen G7 da yake karbar bakuncin taronsu, za su tallafawa kasashen da Gobarar Dajin Amazon ta shafa, cikin gaggawa.

Gobarar dake barazana ga dajin na Amazon dai ta shiga cikin muhimman batutuwan da taron kasashen 7 masu karfin tattalin arziki ke tattaunawa a kai.

Kashi 60 cikin 100 na dajin Amazon din na cikin kasar Brazil ne, sai dai dajin da akai ittifakin shi ne mafi girma a duniya ya ratsa ta cikin Karin kasashe 8 daga cikinsu kuma akwai, Bolivia, Colombia, Peru, Vanezuela da kuma Ecuador.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.