Isa ga babban shafi
Kenya-Moi

Al'ummar Kenya na makokin Daniel Arap Moi

Dubban al’ummar kasar Kenya ne suka yi dafifi a wani katafaren filin wasannin motsa jiki don nuna alhinin mutuwar tsohon shugaban kasar mafi dadewa a karagar mulki, Daniel Arap Moi, a daidai lokacin da ake addu’ar jana’izarsa.

Tsohon shugaban kasar Kenya Daniel Arap Moi.
Tsohon shugaban kasar Kenya Daniel Arap Moi. Reuters/George Mulala
Talla

Kafin ketowar al’fijir a Talatan, nan masu juyayin suka fara tururuwa zuwa wani filin wasannin motsa jiki na kasa don mika gaisuwa ta karshe ga tsohon shugaban kasar wanda ya rasu ranar 4 ga watan Farairu yana da shekaru 95.

Moi ya shafe shekaru 24 yana mulkin kasar Kenya, inda daga karshe ma ya mayar da kasar karkashin jam’iyya daya, kuma a lokacin ne duk wani mai adawa da kane-kane da ya yi a madafun iko ke shan ukuba.

Shugaba Uhuru Kenyatta wadda ya bude wannan addu’ar jana’izar da taken kasar, ya bayyana Moi a matsayin gwarzon Africa baki daya.

Tsohon abokin hamayyarsa, Raila Odinga, wanda ya sha dauri a karkashin mulkin Moi ya bayyana marigayin a matsayin jajirtacce, wanda daga baya ya amince da tsarin jam’iyyu fiye da daya.

Cikin wadanda suka fuskanci ukuba yayin mulkin Moi akwai shahararren marubucin nan, Ngugi wa Thiong'o da takwaransa Wangari Maathai.

An jinjina wa Moi, wanda ya mika mulki cikin ruwan sanyi ga Mwai Kibaki a shekarar 2002, ganin yadda Kenya ta zauna lafiya a lokacin da ya mamaye gabashin Afrika, musammamn kisan kare dangi a Rwanda da yakin basasa a Burundi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.