Isa ga babban shafi
Kenya-Ta'addanci

Kenya ta kame mutane 5 da ke kitsa harin ta'addanci

Mahukuntan Kenya sun sanar da kame wasu mutane 5 da ake zargi da kitsa yadda za su kaddamar da hare-hare a Nairobi babban birnin kasar.

Jami'an tsaron Kenya da ke binciken ababen hawa a shingayen bincike.
Jami'an tsaron Kenya da ke binciken ababen hawa a shingayen bincike. REUTERS/Stringer
Talla

Mutanen 5 da mahukuntan na Kenya ke zargi da zamowa ‘yan ta’adda, jami’an ‘yansandan kasar sun ce sun hadar da maza 3 da suka kunshi Ba’amurke guda dan Somalia guda da kuma Direbansu dan Kenya, kana wasu mata biyu dukkanninsu ‘yan Somalia da ake zargin su ake shirin daurawa bom don kai harin kunar bakin wake.

Rundunar ‘yan sandan Kenya da ta fitar da rahoton kamen mutanen 5 a yau Lahadi, ta ce tun a juma’ar da ta gabata sashen bayanan sirrinta ya gano mutanen da kuma abin da su ke shirin aikatawa.

A cewar rundunar bayan kaddamar da wani sumame ne ta yi nasarar kame mutanen 5 a Kiambu, yankin da ya yi shura wajen tattara batagari a birnin na Nairobi.

Jami’an tsraon Kenya sun kasance a ankare ne tun bayan harin tsagin Al-Shabaab mai biyayya ga Al-Qaeda ranar 5 ga watan nan a sansanin Simba da ya hallaka Amurkawa 3 baya ga lalata tarin kayakin yaki.

Kungiyar dai ta bayyana harin na farkon watan nan a matsayin gargadi ga gwamnatin Kenya da ta aike da dakaru na musamman don yaki da kungiyar Al-shebaab a Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.