Isa ga babban shafi
Kenya

Tsohon shugaban kasar Kenya ya rasu

Tsohon shugaban Kenya Daniel Arap Moi wanda ya jagoranci kasar tsakanin shekarar 1978 zuwa 2002 ya rasu a wannan Talatar yana da shekaru 95 a duniya.

Marigayi tsohon shaugaban kasar Kenya, Daniel Arap Moi
Marigayi tsohon shaugaban kasar Kenya, Daniel Arap Moi ALEXANDER JOE / AFP
Talla

Shugaba Uhuru Kenyatta ya sanar da mutuwar tsohon shugaban wanda ya kwashe shekaru 24 yana mulkin Kenya, inda ya sanar da zaman makoki har zuwa lokacin da za a yi wa Moi jana’iza.

Ana zargin marigayin da mulkin kama-karya lokacin da ya jagoranci kasar, yayin da a bangare daya ake yaba masa wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar, a daidai lokacin da kasashe makwabta irin su Rwanda da Burundi da Somalia ke fama da yakin basasa.

Wani abin da ya mamaye lokacin mulkinsa shi ne bacewar Dala biliyan guda daga Babban Bankin Kasar wajen fitar da gwal da lu’u lu’u na bogi zuwa kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.