Isa ga babban shafi
China-Amurka

China zata wuce Amurka a kasuwar sayar da kayatattun motoci- Bincike

Wani bincike da aka gudanar na nuna cewa kasar China za ta fi kasar Amurka ciniki a kasuwar sayar da kayatattun motoci nan da shekarar 2016. A yanzu haka China ita ce kasa ta biyu a duniya wajen kera iri wadannan motoci bayan kasar ta Amurka, inda ta sayar da motoci miliyan 1.25 a shekarar da ta gabata.  

Sabon Shugaban kasar China Xi Jingping
Sabon Shugaban kasar China Xi Jingping 路透社
Talla

A cewar binciken, wanda Cabiyar hadahadar kasuwanci ta McKinsey & Company ta gudanar, yawan motocin da Chinan ke sayarwa zai iya kaiwa guda miliyan 2.25 a shekarar ta 2016 kana su kuma kai yawan miliyan 3.0 a shekarar 2020.

Kasar Amurkan dai ta sayar da motoci da yawansu ya kai miliyan 1.7 a shekarar da ta gabata ana kuma sa ran hakan zai haura zuwa miliyan 2.3 nan da shekarar 2020.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.