Isa ga babban shafi

Bincike ya nuna Yankin Asiya ya fi sauran Nahiyoyi yawan Attajirai a Duniya

Wata mujallar attajirai a China ta wallafa sakamakon bincikenta wanda yace Yankin Asiya ke da yawan attajirai fiye sauran Nahiyoyin Duniya, kodayake a shekarun baya yankin Arewacin Amurka ne akan gaba.

Attajirin Duniya na kasar Mexico Carlos Slim yana gaisawa da Shugaban Kamfanin Microsoft Bill Gates
Attajirin Duniya na kasar Mexico Carlos Slim yana gaisawa da Shugaban Kamfanin Microsoft Bill Gates REUTERS/Henry Romero
Talla

Mujallar mai suna Hurun tace akwai attajirai 1,453 a fadin duniya wadanda suka mallaki kudi fiye da Dala Biliyan daya nasu na kansu. Amma cikin kason mutanen, Yankin Asiya ke da yawan Attajirai 608, sai yankin Arewacin Amurka mai tarin Attajirai 440 da kuma yankin Turai da ke da yawan Attajirai 324 da suka mallaki Biliyan

Wani sakamakon binciken mujallar Forbes ta Amurka a bara ya nuna cewar attajiran Asiya 315 ne idan aka kwatanta da Attajiran Arewacin Amurka 450 da kuma Attajiran Turai su 310.

Kasashen Amurka da China ne a sahun gaba da yawan Attajirai 408 da kuma 317, sai kasashen Rasha da Jamus da kuma Indiya.

Dan kasar Mexico ne Carlos Slim, mai shekaru 73 na haihuwa shi ne aka bayyana a matsayin Attajirin Duniya wanda ya mallaki tsagwaron kudi Dala Biliyan 66.

Attajirin Amurka Warren Buffett da dan kasar Spain Amancio Ortega su ne a matsayi na Biyu da na uku cikin jerin sunayen attajiran Duniya wadanda suka mallaki kudi Dala Biliyan 58 da Biliyan 55.

Birnin Moscow shi ne aka bayyana a matsatin Birni mai tarin Attajirai 76 a Duniya fiye da Birnin New York da Hong Kong da Beijing da kuma Birnin London a matsayin biranen da ke bi ma Moscow.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.