Isa ga babban shafi
G20

Bill Gates ya yi kiran kasashen G20 kada su manta da kananan kasashe

Bill Gates Mashahurin attajirin duniya mai Kamfanin Microsoft ya yi kiran kasashen G20 masu karfin tattalin arziki kada su manta da kananan kasashe masu karamin karfin tattalin arziki a lokacin da suke kokarin magance matsalar da ta shafi Turai. A lokacin da yake gabatarwa kasashen rehoto kan yaki da talauci Bill Gate yace ya dace a tsaya a diba matsalar kasashe masu fama da talauci domin kare rayuwar kananan yara.Matsalar tattalin arzikin kasashen Turai dai ita ce ta mamaye taron kasashen na G20 amma Bill Gates yace duk da matsalar da ke addabar kasashen Turai ya dace a tuna da kananan kasashe.Kasashen G20 su suka mamaye kashi 85 na tattalin arzikin duniya, sai dai Bill Gates yace suna iya samar da Tallafin kudi sama da Euro Biliyan 250 domin taimakawa kasashe masu fama da talauci.A cewarsa bunkasa Al’umma shi ne zai kawo ci gaban kasa da tattalin arziki, domin wannan abun misali ne idan aka yi la’akari da kasashen China da Indiya da Brazil. 

shugaban kamfanin  Microsoft, Bill Gates, a taron kasashen G20 à birnin  Cannes.
shugaban kamfanin Microsoft, Bill Gates, a taron kasashen G20 à birnin Cannes. REUTERS/Kevin Lamarque
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.