Isa ga babban shafi
Wasanni

Za a soma amfani da fasahar VAR a gasar zakarun Turai - UEFA

Shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA, Aleksander Ceferin, ya ce a wannan makon za a soma amfani da fasahar taimakawa alkalin wasa da maimacin bidiyo wato VAR a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Fasahar taimakawa Alkalin wasa da maimaicin bidiyo VAR.
Fasahar taimakawa Alkalin wasa da maimaicin bidiyo VAR. Reuters
Talla

A baya dai hukumar ta UEFA ta tsara sai a kakar wasa ta badi za a soma amfani da fasahar ta VAR, amma aka sauya shawarar soma amfani da ita a yanzu, watanni 6 kafin wa’adin farko ya cika.

Hakan na nufin fasahar za ta soma aiki a wasannin da za a yi ranar Talata 12 ga Fabarairu tsakanin Manchester United da PSG, da kuma AS Roma da FC Porto.

Manyan gasannin nahiyar Turai sun dade suna kira da a soma amfani da fasahar maimaicin bidiyon, kamar yadda aka yi amfani da ita a gasar cin kofin duniya ta 2018 a Rasha.

Shugaban kungiyar Juventus Adrea Agnelli na kan gaba wajen tabbatar da an soma amfani da fasahar, sakamakon fusatar da yayi da yadda a gasar zakarun nahiyar Turai ta bara, Real Madrid ta fitar da kungiyar tasa, ta hanyar samun damar bugun daga kai sai mai tsaron gida a mintunan karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.