Isa ga babban shafi
Wasanni

FIFA ta hukunta Najeriya saboda karya doka

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta rage yawan makin da Najeriya ta samu a rukuninta na gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya bayan ta samu Super Eagles da laifin sanya Shehu Abdullahi a wasan da ta yi da Algeria a watan jiya.

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta samu nasarar zuwa gasar cin kofin duniya a Rasha
Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta samu nasarar zuwa gasar cin kofin duniya a Rasha REUTERS/Dylan Martine
Talla

FIFA ta ce, Abdullahi bai cancanci buga wannan wasa ba saboda katin gargadi har guda biyu da ke kansa, abin da ke nufin cewa, ya kamata a haramta ma sa buga wasa guda.

Kazalika FIFA ta ci tarar Najeriya Dala dubu 6 da 52 kimanin Naira miliyan 2 da dubu 170.

Sai dai hakan ba zai hana Najeriya zuwa gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha a shekara mai zuwa ba, amma makinta ya koma 11 daga 14, yayin da Algeria ta samu maki 5 a rukunin.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick ya bai wa ‘yan Najeriya hakuri, yayin da ya bayyana laifin a matsayin babban kuskure kuma a cewarsa za su hukunta mai hannu a cikin lamarin.

Yanzu haka FIFA ta ayyana Algeria a matsayin wadda ta lallasa Najeriya da kwallaye 3-0 duk kuwa da cewa sun tashi ne 1-1 a wasan wanda suka yi a ranar 10 ga watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.