Isa ga babban shafi
Faransa

Tsohon shugaban Faransa Sarkozy zai gurfana gaban kotu

Ma’aikatar shari’ar kasar Faransa ta tuhumi tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy da cin hanci da rashawa da kuma karbar kudaden yakin neman zabe daga hannun tsohon shugaban kasar Libya Muammar Ghadafi ta hanyar da ba ta kamata ba domin yakin neman zabensa na shekarar 2007.

Tsohon shugaba Nicolas Sarkozy, da takwaransa Mouammar Kadhafi ranar 25  watan yulin 2007.
Tsohon shugaba Nicolas Sarkozy, da takwaransa Mouammar Kadhafi ranar 25 watan yulin 2007. REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Bayan shekaru 5 ana gudanar da bincike da kuma kwashe kwanaki biyu ana yi wa tsohon shugaban tambayoyi, alkalan da ke sa-ido kan wannan badakala ta karbar kudade da ake zargin tsohon shugaban kasar, sun ce akwai isassun shaidun da ke bayar da damar gurfanar da shi gaban kotu.

Masu gabatar da kara sun tuhumi Sarkozy da laifin cin hanci da karbar haramtatun kudade domin yakin neman zabe da kuma boye kudin jama’ar Libya.

Tsohon shugaban, ya ki amincewa da zargin da ake masa, yayin da kotu ta bayar da umurnin ci gaba da sanya ido akan sa duk da ya ke an bar shi ya koma gida daga hannun ‘Yan Sanda.

Sarkozy na da watanni shida domin daukaka kara kan tuhumar, yayin da alkalai ke da damar sake nazari domin cigaba da shari’ar ko kuma watsi da ita.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.