Isa ga babban shafi
Faransa

Zan ci gaba da tsoma baki a siyasa- Hollande

Tsohon Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce babu abin da zai sa ya dakatar da shiga harkokin siyasa a kasar kuma zai ci gaba da tsokaci kan batutuwan da suka shafi kasar lokaci zuwa lokaci.

Tsohon shugaban Faransa François Hollande
Tsohon shugaban Faransa François Hollande Yohan BONNET / AFP
Talla

A wata hira da ya yi da tashar talabijin din TV5, Hollande ya ce lokacin da ya ki gabatar da kansa a matsayin dan takarar zabe wa’adi na biyu, akwai hatsarin da ya hango a gaba, amma kuma hakan ba zai sa ya bar harkokin siyasa baki daya ba.

Hollande ya janyo hankalin shugaba Macron da kar ya tilastawa Faransawa akan bukatunsa na sauye sauyen da ya ke son ya kawo.

Macron dai tsohon minista ne a gwamnatin Hollande kafin ya fice daga gwamnatin ya kafa sabuwar jam’iyyar da ya lashe zaben shugaban kasa.

Tsohon shugaban ya yi gargadi ga Macron akan manufarsa ta sauya tsarin kwadago a Faransa da kuma batun rage kashe kudade a kasafin kudin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.