Isa ga babban shafi
Faransa

Macron na shirin ganawa da 'yan kwadagon Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na shirin ganawa da shugabannin Kungiyoyin kwadago da shugabannin ma’aikatu don tattaunawa alkiblar gwamnatinsa game da sauye-sauyen da zai yi ta fannin kwadago.

Wani lokaci a yau ne shugaban Faransa Emmanuel Macron zai gana da shugabannin 'yan kwadago a Faransa
Wani lokaci a yau ne shugaban Faransa Emmanuel Macron zai gana da shugabannin 'yan kwadago a Faransa REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

A wani lokaci da ake kukan rashin ayyukan yi, wanda ya kai kusan kashi 10 daga cikin 100, kuma ana ganin ganawar za ta kara wa ma'aikatu karfin guiwa wajen diba da korar ma'aikata, da kuma ba su damar tsare-tsaren da suka dace da ayyukansu.

A yayin yakin neman zabensa, Emmanuel Macron ya bayyana cewa zai nemi izimin Majalisar kasar don ganin an zartas da dokoki da suka shafi kwadago ba tare da jibin goshi ba.

Ana sa ran yau Emmanuel Macron ya gana da manyan kungiyoyin kwadago 4 na Faransa domin ganin ya gabatar masu da tsarinsa na tafiya tare da ma'akata.

A cewar shugaban na Faransan, da kansa ne zai sa idanu wajen aiwatar da dukkan sauye-sauye ta fannin kwadago, wanda ya ke cikin daya daga cikin alkawuransa 6 a lokacin yakin neman zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.