Isa ga babban shafi
Syria

Za a tallafawa Syria da Dala miliyan 260

Sama da Dalar Amurka miliyan dari biyu da sittin aka yi alkawarin tarawa don tallafawa Syria da kayyakin agaji ga mabukata da ke cikin kuncin rayuwa sanadiyar yakin basasa na fiye da shekaru shida.

Za a tallafawa Syria da Dala miliyan 260 don samarwa al'umma kayayyakin agaji.
Za a tallafawa Syria da Dala miliyan 260 don samarwa al'umma kayayyakin agaji. Reuters/Majed Jaber
Talla

An cimma wannan matsaya ne bayan kammala taron kasashen Larabawa da ya gudana a kasar Jordan inda Majalisar Dinkin Duniya da wasu kasashe ashirin da biyar na yankin Larabawan suka yi alkawarin tallafawa kasar ta Syria da ta rasa rayukan mutane fiye da dubu dari uku.

Ahmed bin Mohammed Al-Muraikhi wakilin Hukumar agajin gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya ya sanarwa mahalartar taron cewa ana bukatar akalla dala biliyan takwas don samarwa Syria kayayyakin agaji a bana.

An dai yi zaton taron zai samo hanyar kawo karshen yakin basasar da ya haifar da matsalar ‘yan gudun hijra mafi muni a tarihi.

Duk wannan na zuwa ne gabanin soma taron Kungiyar Tarrayar Turai na kwanaki biyu a wannan makon mai kamawa a kasar Belgium kan rikicin na kasar Syria.

Karfin ikon Kungiyoyin 'yan tawaye musanman mayakan jihadi na ISIL a manyan biranen kasar ya matukar jefa al'umma cikin bala'i na rashin ababen more rayuwa da kuma kayyayakin agaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.