Isa ga babban shafi
Hungary

Hungary ta sanya shingen karfe domin hana 'Yan cirani shiga kasar

An kammala sanya wani shingen karfe mai kaifi tsakanin kasar Hungary da kasar Serbia domin hana baki ‘Yan ci rani shiga kasar.

shingen karfe
shingen karfe Ongayo/CC/Wikimedia
Talla

Ma’aikatar tsaron kasar ta Hungary ce ta sanar da hakan, kwanaki biyu kafin cikar wa’adin ranar 31 ga watan Agusta da ta shirya na kammala aikin.

Shi dai wannan shinge mai nisan kilomita 175 yana da karafa masu kaifin reza wanda kan iya yanka mutum, kuma tsayin sa ya kai kafa 13.

Wannan dai yana a matsayin mataki ne da kasar ta Hungary ta dauka domin hana daruruwan ‘Yan cirani dake sha'awar  shiga kasar a kowacce rana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.