Ana zanga-zangar adawa da gwamnati a Hungary
Dubban Mutane ne suka gudanar da wata zanga-zanga a kasar Hungary, domin adawa da shirin Gwamnati na amincewa da wasu sabbin dokoki da suke ganin sun sabawa kundin tsarin mulkin kasar.
Wallafawa ranar:
Sabbin dokoki tuni suka fara aiki daga ranar daya ga watan Janairu, abinda ‘Yan kasar suka ce ba zasu amince da shi ba.
A shekarar 2010 ne Viktor Orban ya samu rinjayen kuri’u a Majalisar kasar wanda ya ba shi mukamin Fira minista, kuma tun a lokacin yake aiwatar da sabbin sauye sauye inda yake fuskantar suka da kalubale daga cikin kasar da wajenta.
Daruruwan ‘’yan kasar ne kimanin 30,000 suka yi gangami a a fadar Budafest domin adawa da gwamnatin Fidesz da sabbin sauye sauyen gwamnatinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu