Tambaya da Amsa
Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Hukumar samar da wutar lantarki ta yi bayani game da kudin wuta da jama'a za su biya a Najeriya
‘Tambaya Da Amsa’ shiri ne da ke kawo amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana. Bayan janye tallafin lantarki a Najeriya, hukumar samar da wutar ta yi bayani game da rukunnai dabam dabam na masu amfani da wuta da abin da za su biya a matsayin kudin wuta. A yi mun ƙarin bayani a kan wadannan rukunnai. Menene ya sa dole sai an kasa al’umma zuwa rukuni -rukuni?13/04/202420:01 -
Ƙarin bayani kan yakin duniya da yadda za'a kauce wa sake barkewarsa
Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon tare da Micheal Kuduson ya amsa wasu daga cikin tambayoyi da masu sauraro suka aiko mana ciki harda amsar tambaya da ke neman bayani a kan yakin duniya da yadda za a kauce wa aukuwar wani yakin duniya.30/03/202420:01 -
Sanadin katsewar kafofin sadarwa na Internet a nahiyar Afirka
shirin a wannnan mako zai ba da hankali ne akan abinda ya kai ga katsewar hanyoyin sadarwa na internet a wasu sassa na Nahiyar Afirka.23/03/202420:00 -
Karin bayani a kan ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol
Shirin yana zuwa muku ne da amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa mukua wannan tasha kuma a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, za mu ji karin bayani a kan ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol. Abokinku, Michael Kuduson ne ke muku lale marhabun.16/03/202420:01 -
Neman bayanni a game da mayar da kasa saniyar ware
Kamar yadda muka saba, shirin yana zuwa muku ne da amsoshin tambayoyin da masu sauronmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa muku a wannan tasha kuma a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman bayanni a game da mayar da kasa saniyar ware, da kuma tasirin haka a kan kasar da aka maida saniyar ware.09/03/202420:00 -
Amsoshin wasu daga cikin tambayoyin masu saurare daga Rfi
A cikin shirin na wannan mako,Michael Kuduson ya duba wasu daga cikin tambayoyin,ko wadanan hanyoyi ne ake bi domin samun tikiti kujerar wakili a Kwamity tsaro na MDD.Ya kuma duba wasu tambayoyi da suka jibanci bangaren tsaro da sauren su.02/03/202420:00 -
Tarihin yan tawayen Houthi na Yemen
A cikin shirin tambaya da amsa na wannan mako, Michael Kuduson ya mayar da hankali a tambayar da ta shafi yan Tawayen Houthi na kasar Yemen.Sai ku biyo mu.17/02/202420:00 -
Tambaya da Amsa: Cikakken tarihin Hausawa 'yan asalin kasar Mali
Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman sanin tarihin Hausawa ‘yan asalin kasar Mali.10/02/202420:00 -
Ko me ya sa gwamnonin jihohi a Najeriya ba su da iko a kan jami’an tsaro?
Shirin ‘Tambaya Da Amsa’ yana kawo muku amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana ne, kuma duk mako yake zuwa muku a daidai wanna lokaci, kuma a wannan tasha. Ko me ya sa gwamnonin jihohi a Najeriya ba su da iko a kan jami’an tsaro? Wannan tambayar na daya daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau. Sai ku kasance tare da abokinku, Michael Kuduson.03/02/202420:00 -
Neman karin bayani a kan Somaliland da ko kasa ce mai ‘yanci?
Shirin ‘Tambaya Da Amsa’ yana zuwa muku ne da amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da wsu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana, kuma duk mako ya ke zuwa muku a daidai wannan lokaci.Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman karin bayani a kan Somaliland da ko kasa ce mai ‘yanci. Sai a biyo27/01/202420:00 -
Bayani a kan ramukan sararin samaniya (Black Holes)
Kamar yadda aka saba, shirin yana kawo muku amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana ne, kuma duk mako yake zuwa muu a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa, akwai wadda ke neman bayani a kan ramukan nan da ke sarari, wadanda ake kira ‘black holes.20/01/202419:59 -
Dalilan da suka hana kasashe masu tasowa dogaro da kansu a bangaren tsaro
Shirin ‘Tambaya Da Amsa ‘ yana zuwa muku ne kowane mako a wannan tasha, inda ya ke kawo amsoshin tambayoyin da suka samu shiga daga masu sauraronmu. Daga cikin tambayoyi da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman bayani a kan dalilin da ya sa kasashe masu tasowa ba iya dogaro da kan su wajen yaki da matsalar tsaro,, musamman ma ta’addanci da sauransu.16/12/202319:58 -
Bayani a kan masu 'kujerar naki' a Majallisar Dinkin Duniya
Shirin 'Tambaya Da Amsa' na wannan mako kaamar kowane mako, ya kawo muku tambayoyi ne da masu sauronmu suka aiko mana, inda ya samar da amsoshinsu daidai gwargwadon iko. Daga cikin tambayoyin da muka amsa a yau, akwai wadda ke neman sanin yadda aka yi wasu kebabbun kasashe suka samu "kujerar naki' a Kwamitin Tsaro nna Majalisar Dinkin Duniya.18/11/202320:00 -
Tambaya dangane da bayani a kan kisan kare dangin Holocaust
Tambaya daga Alhaji Haruna Kira da Umar Ladan Baturiya daga jihar Jigawa Najeriya. So suke a banbanta musu tsakanin ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga. Ko akwai dokar da ke hana amfani da karfi fiye da kima a kan irin wadannan masu aikata manyan laifuka?11/11/202320:00
Tambaya da Amsa
Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.