Isa ga babban shafi
Najeriya-Abuja

'Yan sanda sun watsa taron mabiya Shi'a a Abuja

Yan Sanda a Najeriya sun watsa taron tattakin ‘yan Shi’a a gaf da kasuwar Wuse dake Abuja.

Wasu mambobin kungiyar Shi'a a Najeriya lokacin da su ke zanga-zangar neman ganin an saki shugabansu Ibrahim Zakzaky. 11/7/2019.
Wasu mambobin kungiyar Shi'a a Najeriya lokacin da su ke zanga-zangar neman ganin an saki shugabansu Ibrahim Zakzaky. 11/7/2019. REUTERS/Abraham Achirga
Talla

Rahotanni sun ce ‘ya ‘yan kungiyar ‘yan uwa Musulmin ta Shi’a sun soma gangamin ne a matsayin sharar fage na tattakin da za su yi a ranar asabar, domin alhinin zagayowar cika kwanaki 40 da kisan gillar da aka yiwa Imam Hussein.

Sai dai jim kadan bayan soma tattakin na wannan Juma’ar ne, ‘yan sanda suka watsa gangamin ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma harbi cikin iska.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sha nanata cewar haramun ne ‘yan kungiyar ta Shi’a su rika gudanar da gangami, bayan da kotu ta haramta ayyukansu a watannin baya.

Matakin haramta ayyukan mabiya Shi’a a Najeriya ya biyo bayan arrangamar da aka samu a lokuta mabanbanta tsakaninsu da jami’an tsaro, yayinda suke gudanar da zanga-zangar neman sakin jagoransu Shiekh Ibrahim El Zakzaky da mai dakinsa Zeenatu, da gwamnati ta tsare tun a shekarar 2015, bayan arragamar mabiyansu da sojoji a Zaria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.