Isa ga babban shafi
kamaru

HRW ta zargi sojin Kamaru da cin zarafin fararen hula

Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta Human Right Watch ta zargi jami’an tsaron Kamaru da aikatan munanan laifukan cin zarafi kan fararen hula, inda ta ce, sojojin kasar sun kashe mutane hudu da kuma yi wa wata mata fyade a yankin masu magana da Turancin Ingilishi a kasar.

Wasu daga cikin sojojin Kamaru
Wasu daga cikin sojojin Kamaru REUTERS/Joe Penney
Talla

Kimanin shekaru uku kenan da dakarun gwamnatin Kamaru ke yaki da ‘yan awaren da ke neman ballewa daga kasar domin cin gashin kansu a yankunan arewa maso yammaci da kuma kudu maso yammacin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane tare da tilasta wa akalla mutane dubu 500 kaurace wa muhallansu.

Kungiyar Human Right Watch ta ce, wani dattijo mai shekaru 80 da kuma wani matashi mai fama da larurar tabin hankali na cikin wadanda aka hallaka a yayin wani samamen sojoji a cikin tsakiyar watan Yunin da ya gabata.

Kungiyar ta bakin Darektanta na Tsakiyar Afrika, Lewis Mugde ta ce, wannan laifin na baya-bayan nan, ya dada fito da irin cin zarafin da sojoji suka yi wa fararen hula.

A cewar Kungiyar, wata mata mai shekaru 40, ta sha dukan tsiya da kuma yi mata fyade a wani ban-daki da ke garin Kumba a ranar 21 ga watan Yuni bayan wani gungun sojoji ya bukaci sanin maboyar ‘yan awaren kasar.

A maimakon daukar matakin tabbatar da shari’a kan masu laifin, gwamnatin Kamaru ta musanta cewa, sojojinta sun aikata kisa da fyade in ji Kungiyar ta Human Right Watch wadda ta ce, tana tunatar da gwamnatin kasar cewa, duniya na kallon ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.