Yanzu haka ‘yan Najeriya na cigaba da bayyana ra’ayoyi daban daban kan rikicin da aka samu na baya bayan nan a Jihar Filato wanda yayi sanadiyar hallaka rayukan mutane da dama.Wannan ya sa wasu suka fara nuna yatsa ga gwamnatin jihar kan kasa daukar matakn da suka dace na kawo karshen rikicin.Ministan matasa da wasanni Barr Solomon Dalung wanda ya fito daga Jihar ya bayyana ra’ayin sa akai a tattaunawar da suka yi da wakilinmu dake Abuja Muhammad Sani Abubakar.
Sauran kashi-kashi
-
Bashir Dan-Malam kan karancin man fetur a sassan Najeriya
Rahotanni daga sassan arewacin Najeriya na nuna cewar an fara samun karancin mai a gidajen mai, abinda ya sa wasu masu man suka kara farashin da suke sayar da kowacce lita.25/04/202403:16 -
Arewa maso Yammacin Najeriya ne mafi hatsari saboda matsalar tsaro - Bincike
Kungiyar 'Global Rights' ta bayyana yankin arewa maso yammacin Najeriya a matsayin mafi hadari, saboda yadda 'yan bindiga ke kisa da take hakkin Bil Adama ba tare da kaukautawa ba.18/04/202403:16 -
Kuskure ne a yi tunanin ɗagawar darajar naira ba zai ɗore ba - Dakta Kurfi
Darajar Naira na cigaba da ɗagawa a Najeriya tare da saukar farashin wasu kayayyakin abinci a wasu kasuwannin ƙasar, abinda ya sa wasu tunanin cewar tasirin saukar Dalar ne ya sanya wasu kayayyakin suka fara sauka.17/04/202403:19 -
Tattaunawa da Sanata Ikira Aliyu Bilbis kan tsaro a jihar Zamfara
Hukumomi a Najeriya daga matakin jiha zuwa na kasar baki ɗaya na daukar matakai daban daban wajen samar da zaman lafiya a jihar Zamfara, amma har ya zuwa wannan lokaci ba'a kai ga cimma biyan bukata ba.16/04/202403:26 -
Yadda rayuwa ta kasance bayan da muka faɗa hannun mayakan Boko Haram - Maryama
A ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilun nan aka cika shekaru 10 da sace dalibai mata na makarantar sakandaren Chibok sama da 250 da mayakan Boko Haram suka yi a jihar Borno.15/04/202403:17