Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun kama mutane 72 a Jos

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kame akalla mutane 72 a garin Jos dake jihar Filato, bayan kaddamar da binciken da tayi kan mutuwar tsohon hafsanta Janar Idris Alkali, wanda aka gano motarsa a wani kududdufi dake yankin ‘Du’ a karamar hukumar Jos ta Kudu.

Daya daga cikin karin motocin da sojin Najeriya suka gano a kududdufin yankin Du dake garin Jos.
Daya daga cikin karin motocin da sojin Najeriya suka gano a kududdufin yankin Du dake garin Jos. Premium Times Nigeria
Talla

Kwamandan rundunar sojin Najeriyar ta musamman 'Operation Safe Haven, Manjo Janar Augustine Agundo, ya shaidawa manema labarai a garin Jos cewa, zuwa yanzu, 30 daga cikin mutane 72 da suka kama ne kawai suka amsa laifukan da ake zarginsu da aikatawa.

A ranar Larabar nan da ta gabata hedikwatar sojin Najeriya ta sanar da kame wasu mutane 30, biyo bayan kaddamar da binciken, wanda ya zama karo na farko da ta soma daukar matakin, tun bayan rasa hafsanta Janar Idris Alkali.

Daga cikin abubuwa da sojin suka gano tattare da mutanen da ake zargi, akwai, bindigogi kirar gida guda shida, manya da kanana, sai kuma wukake da adduna.

Sauran kayayyakin sun hada takalman soji, katunan shiadar jami’an Vigilante 3, baburan hawa 5, da kuma babur mai kafa 3 daya.

Kamen da sojin na Najeriya suka yi, ya zo ne bayan sanar da gano wasu karin motoci hudu a cikin tafkin da ake bincike akai, domin gano gawar tsohon Janar Idris Alkali da ake zaton wasu ‘yan bindiga sun hallaka shi a ‘Doi Du’ dake karamar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.

Babban hafsan dake jagorancin aikin binciken, Manjo Janar Augustine Agundo yace ba za suyi kasa a gwuiwa ba wajen cigaba da gudanar da ayyukan su har sai sun cimma nasara.

Gudanar da wannan bincike ya biyo bayan zargin hallaka Janar Idris Alkali, tsohon babban hafsan sojin Najeriya, da ake zargin wasu ‘yan ta’adda da aikatawa a yankin na ‘Doi Du’.

Yayin gabatar da nasarar da suka samu, Manjo Janar Agustine Agundu, yace yanzu haka sun ciro motoci guda 3 da kuma wasu tarin kayayyaki na bam mamaki.

Kwamandan runduna ta 3 na sojin Najeriya dake da Cibiya a birnin Jos, Manjo Janar Benson Akinruluyo yace zasu cigaba da aikin su har sai sun ga abinda ya turewa buzu nadi.

A wata hira da yayi da manema labarai, Gwamnan Jihar Plateau Simon Lalong ya sha alwashin daukar mataki mai tsauri kan masu tare hanya suna kashe mutane a Jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.