Isa ga babban shafi
Najeriya

Mahara sun kashe mutane 10 a daren jiya a jihar Bebue

A Najeriya akalla mutane 10 ne suka mutu a yayin da ‘yan Bindiga suka kai wa wasu kauyuka hari a jihar Benue.

Mace dauke da danta a sansanin 'yan gudun hijira na jihar Benue
Mace dauke da danta a sansanin 'yan gudun hijira na jihar Benue REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo
Talla

Mazauna kauyukan karamar hukumar Guma sun tabbatarwa manema labarai cewar hakika maharan da suka yi sammakon kai wa al’ummar kauyukan hari sun kashe mutane 10 tsakanin daren Jumu’a wayewar safiyar yau Assabar.

Mai magana da yawun Gwamnan jihar ta Benue Terver Akase ya tabbatar cewar an samu kwashe gawawwaki akalla 10 a harin da suke zargin wata kabila da kai wa, da kuma maharani suka kona gidaje da dama.

Ya yi kira ga jami’an tsaron kasar da su tabbatar sun kama wadanda ake zargi da kai harin domin samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar manoma da kuma makiyaya.

Dam adai an dade ana zaman dar dar tsakanin al’ummar jihar ta Benue da Fulani makiyaya da ke kula da dabbobinsu a jihar da ke a yankin Arewa ta tsakiyar Najeriya .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.