Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya yi alla-wadai da hare-haren jihar Benue

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nuna bacin ransa dangane da hare-haren da aka kai jihar Benue wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jajantawa al'umma da kuma gwamnan jihar ta Benue dangane da hasarar rayukan da kuma dukiya, da hare-haren suka haddasa.

Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Makurdi, inda suka yi kira ga gwamnati ta dauki matakan da suka wajaba domin dawo samar da tsaro a yankin.

Zanga-zangar ta biyo bayan kisan wasu mutane akalla 20 tare da raunata wasu kimanin 30, a wani hari da ke zaton makiyaya ne suka kai a kananan hukumomin Guma da Logo da ke jihar Benue a tsakanin ranakun Litinin da Talata da suka gabata.

Sai dai rundunar ‘yan sandan kasar ba ta kai ga tabbatar da yawan wadanda suka rasa rayukan nasu a hukumance ba.

Domin samun karin bayani kan wannan rikicin ne, Sashin Hausa na RFI ya tuntubi Ali Teshako, mai bai wa gwamnan jihar Benue Samuel Ortom shawara kan sha’anin tsaro, wanda ya bayyana cewa rikicin yana tattare da makarkashiyar wasu bata gari da basa son zaman lafiyar al’umma.

Dangane da dokar haramta kiwo a jihar da gwamnatin Benue ta kafa kuwa, Teshako ya ce, dokar ta yi tasiri matuka wajen rage yawaitar barkewar rikici tsakanin manoma da makiyaya.

00:38

Ali-Teshako-2018-01-04

Abdoulkarim Ibrahim

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.