Isa ga babban shafi
Najeriya

Gonakin Shinkafa sama da 400 sun nutse cikin ambaliyar ruwa

Akalla gonakin Shinkafa dari hudu da hamsin da takwas (458) ne suka nutse cikin ambaliyar ruwan da ta shafi wasu daga cikin sassan jihar Kwara, a Najeriya.

Ambaliyar ruwa ta salwantar da daruruwan gonakin Shinkafa a jihar Kwara.
Ambaliyar ruwa ta salwantar da daruruwan gonakin Shinkafa a jihar Kwara. REUTERS/Navesh Chitrakar
Talla

Gonakin da ke karamar Shonga Edu a jihar suna karkashin sabon shirin gwamnatin Najeriya ne na 'Anchor Borrower' na tallafawa manoman shinkafa, karkashin jagorancin Babban Bankin Kasar CBN.

A cikin watan Oktoba mai zuwa ne ake sa ran girbe shinkafar da aka shuka a gonakin kafin aukuwar wannan iftila’in.

Gwamnan jihar ta Kwara AbdulFatah Ahmed wanda ya ce naira miliyan Dari Bakwai da Ashirin aka ware domin gina kariya ga gonakin daga ambaliyar ruwa, ya bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta daukar matakan taimakawa manoman da iftila’in ya rutsa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.