Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Kai mana hari ba zai razana mu ba’

Mukaddashin shugaban Hukumar da ke yaki da rashawa a Najeriya, EFCC, Ibrahim Magu ya ce babu abinda zai razana su dangane da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai ofishin su da ke Abuja

Mukaddashin shugaban Hukumar da ke yakar Rashawa EFCC Ibrahim Magu a Najeriya
Mukaddashin shugaban Hukumar da ke yakar Rashawa EFCC Ibrahim Magu a Najeriya premiumtimesng.com
Talla

A tattaunawarsa da RFI Hausa, Magu, ya ce wannan hari zai dada karfafa musu gwiwa kan ayyukan da suke yi na kwato dukiyar talakawa da barayi suka yi rub da ciki a kai.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun kai harin ne da misalin karfe 5 na Asuban Laraba, inda suka bude wuta kan ofishin da ke unguwar Wuse, suka kuma lalata motoci kafin jami’an hukumar su kore su.

Kazalika Maharan Sun ajiye wasikar barazana a gini Hukumar.

Ofishin EFCC da ke Wuse ne ke da alhakin binciken laifufukan da suka shafi halarta kudaden haramun a karkashin Ishaku Sharu.

Yanzu haka dai ofishin na gudanar da bincike kan mutane da dama cikin su harda ‘yan siyasa da ake zargi da aikata irin wadanan laifufuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.