Isa ga babban shafi
Wasanni-Najeriya

Dan Kenya ya lashe gasar tseren gudun dogon zango a Legas

‘Yan wasan tsere na dogon zango a Najeriya, sun dora alhakin rashin tabuka abin azo a gani da suka yi, a gasar tseren da ta gudana a birnin Legas a ranar Asabar din da ta gabata kan rashin kyakkyawan shiri. 

Abraham Kipton da ya lashe gasar tseren gudu na dogon zango da ta gudana a Legas
Abraham Kipton da ya lashe gasar tseren gudu na dogon zango da ta gudana a Legas
Talla

‘Yan wasan sun ce babu yadda za’a yi a biyo su har gida a lashe wannan gasa da a ce suna fafatawa a ire-irenta a lokuta daba daban.

Magujin kasar Kenya Abraham Kiptum ne ya kare kambunsa da ya lashe a shekarar da ta gabata ta 2016, sakamakon nasarar da ya samu a gasar tseren gudun na dogon zango.

Dan Najeriya da ya yi nasarar zama na farko da ya kammala tseren a tsakanin ‘yan kasar, Iliya Pa, ya bayyana rashin jin dadinsa bisa yadda suka gaza samun galaba a gasar, inda ya shawarci gwamnatin Najeriya ta rika shirya makamanciyar gasar akai akai domin kara kwazon ‘yan kasar ta hanyar samun yawan atasaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.