Ana ci gaba da gwabza fada tsakanin mayakan Yemen da al'umar yankin
Sama da 'yan tawaye da sojojin gwamnati 140 suka mutu a kasar Yemen cikin wannan makon yayin da ake ci gaba da gwabza fada a garin Marib na arewacin Yemen mai muhimmanci ga bangorin biyu.
Wallafawa ranar:
Majiyoyin soji da na lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, an kashe aƙalla sojojin gwamnati 51 a cikin kwanaki huɗu da suka gabata, akasarinsu a rikicin da aka yi a lardin Shabwa da yankuna dake makwabtaka da Marib.
Yayin da aƙalla 'yan tawayen Huthi 93 da Iran ke marawa baya suma suka mutu fadace-fadacen da kuma hare-haren sama da kawancen sojojin da Saudiyya ke jagoranta ke marawa gwamnati baya ke kai musu
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu