Isa ga babban shafi
Amurka

Gobarar daji a Amurka ta kone fadin kasa mai yawan gaske

Mahaukaciyar gobarar daji a Amurka, na cigaba da kone fadin kasa mai yawan gaske a sassan jihohin California, Washington da kuma Oregun, inda a nan kadai gobarar ta tashi garuruwa 5 bayan tilasta kwashe kimanin mutane dubu 500 daga muhallansu.

Wutar daji a yankin California na kasar Amurka
Wutar daji a yankin California na kasar Amurka REUTERS/Stephen Lam
Talla

Gobara dajin na cigaba da tada kauyuka a jihohi shida na kasar Amurka a yayin da ma’aikatan agaji da yan kwana kwana suke kwashe jama’a.

Hukumomi sun tabatar da mutuwar mutane bakwai a jihohin da suka hada da California washington da oregon.

Akwai wuraren da ba a san halin da ake ciki ba wanda yake nuna yawan wadanda suka mutu yana iya karuwa.

A kalla garuruwa biyar suka kone kurmumus a sanadiyar wutar dajin. Kuma ana ci da kwashe mutane kamar yanda Gwamnan jihar Oregon Kate Brown ya sheidawa manema labarai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.