Isa ga babban shafi
Duniya

Amurka ta zargi kasashen China da Rasha da Iran da yiwa zaben ta zagon kasa

Babban Jami’in leken asirin Amurka, William Evavina ya zargi kasashen China da Rasha da kuma Iran da yunkurin yiwa shirin zaben shugaban kasar da za’ayi a watan Nuwamba zagon kasa.

Wasu daga cikin ma'aikatan hukumar zabe
Wasu daga cikin ma'aikatan hukumar zabe RAYMOND ROIG / AFP
Talla

Sanarwar da Daraktan ya gabatar tace kasashen na yin amfani da matakai na boye da bayyane wajen dauke hankalin masu kada kuri’u a zaben mai zuwa.

Daraktan yace China bata bukatar ganin shugaba Donald Trump ya samu nasarar cigaba da zama a karagar mulki, yayin da Rasha ke neman yiwa Joe Biden zagon kasa.

Jami’in ya ce bukatar Iran itace yin zagon kasa ga shirin baki daya da kuma rarraba kan al’ummar kasar wajen yada bayanan karya ta kafofin intanet.

Shugabannin hukumomin tsaron Amurka sun zargi Rasha da sanya hannu wajen zaben shekarar 2016 wanda shugaba Trump ya samu nasara, duk da yake kasar taki amincewa da zargin.

Wannan zargi na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Donald Trump ke bayyana shakku kan sahihancin zaben da ake aikawa da gidajen waya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.