Isa ga babban shafi
UN

Yin amfani da gidan sauro shine hanyar magance matsalar cutar Malaria – Inji UNICEF

Hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya, ta UNICEF, ta ce yin amfani da gidan sauro itace hanyar da za a iya rage mace mace da rashin lafiya dake aukuwa sanadiyar cizon sauro. Zazzabin cizon saura ko kuma Malaria na sanadiyar mutuwar mutane sama da 600,000 a kowace shekara, aksarinsu yara kanana kuma daga Nahiyar Afrika, inji hukumar Kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta UNICEF. 

Ana koyar da mutane yadda ake yin amfani da gidan sauro domin kariya daga cizon sauro
Ana koyar da mutane yadda ake yin amfani da gidan sauro domin kariya daga cizon sauro Georges Merillon/Global Fund
Talla

Hukumar ta yi wannan bayani a yayin da ake yin bukin tunawa da ranar yin yaki da cutar Malaria ta duniya.

Hukumar ta kara jaddada cewa yin amfani da gidan sauro mai dauke da magani shine ingantacciyar hanyar da zai iya rage adadin wadanda ke mutuwa ta sandiyar cutar ta Malaria.

A cewar UNICEF, a shekarar 2004, adadin ragar sauro a duk fadin Nahiyar Afrika bai wuce guda miliyan 5.6, sai dai hadin gwiwar da kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi suka yi a matakai daban daban, a shekarar 2010, ya sa an sami karuwar yawan ragar sauran.

Hukumar ta kara da cewa yin amfani da ragar ta sauro wacce ke dauke da magani za ta iya rage mace macen yara da kasha 20 cikin 100 a duk shekara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.