Isa ga babban shafi
Cyprus

Shugaban babban bankin Cyprus Andreas Artemis ya ajiye mukaminsa

Shugaban babban bankin kasar Cyprus, Andreas Artemis ya ajiye mukaminsa a dai dai lokacin da kasar ke yunkurin neman tallafi daga kasashen duniya domin ceto tattalin azrikin kasar da ya shiga wani hali. Kamfanin Dallancin labarai na kasar ta Cyprus, ya bayyana cewa za a aika da takardar ajiye aikin nasa gaban gaban kwamitin bankin nan ba da jimawa ba.  

Shugaban babban bankin kasar Cyprus, Andreas Artemis
Shugaban babban bankin kasar Cyprus, Andreas Artemis greece.greekreporter.com
Talla

A jiya Litinin ne kasar Cyprus ta kulla yarjejeniya da Kungiyar Tarayyar Turai inda za a tallafawa kasar da kudin Euro biliyan 10.

Bayanai na nuna cewa Artemis ya kuma ajiye mukamin nasa ne saboda sharuddan da aka gindaya na karbar bashin ceto babban bankin kasar.

Dukkanin bankunan Cyprus dai sun kasance a rufe tun bayan kulla wannan yarjejeniya, inda ake sa ran za su kwashe kwanaki 11 kamin su bude.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.