Isa ga babban shafi
India

Mutumin da ake zargi da laifin fyade da kisa ya mutu ne ta hanyar rataya – Rahoto

Binciken farko da aka gudanar akan mutuwar mutumin nan da ake zargin ya jagoranci yin fyade da kisan kai akan wata daliba a kasar India na nuna cewa ya mutu net a hanyar rataya.

Motar dake dauke da wadanda ake zargi da yin fyade ga wata daliba, akan hanyarsu ta zuwa gidan yari
Motar dake dauke da wadanda ake zargi da yin fyade ga wata daliba, akan hanyarsu ta zuwa gidan yari REUTERS/Stringer
Talla

A ranar Litinin din da gabata ne aka tsinci Ram Singh, wanda yana daya daga cikin mutane shida da ake zargi da laifin yin fyade da kisa a mace a cikin dakin day a ke tsare a gidan yarin Tihal.

‘Yan uwan Singh na zargin cewa kashe shi aka yi.

A daya bangaren kuma mahaifiyar dalibar da aka kashe na zargin ‘Yan sanda da yin sakaci wajen kare Singh ganin cewa shine jagoran wanda ya yi sandiyar mutuwar ‘Yarta, wacce har izuwa yanzu ba a ambaci sunanta ba.

A gobe Laraba ne ake san ran za a gabatar da rahoton binciken a gaban kotu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.