Isa ga babban shafi
MDD

Akwai karanci abinci da ruwan sha a duniya, inji MDD

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya yace akwai karancin abinci da ruwan sha da kayan more raruwa a duniya, inda majalisar ta yi gargadin cewa akwai bukatar kasashen duniya su bada karfi wajen samar da abinci domin gudun kada miskinai da fakirai su yawaita a duniya.

Wata Yarinya dauke da kwanon ruwan sha a Najeriya tana sayarwa
Wata Yarinya dauke da kwanon ruwan sha a Najeriya tana sayarwa REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya na cewa idan aka yi sakaci da lamarin abinci, ruwansha da wuta, a duniya, mutanen da zasu shiga halin ni ‘yasu zasu kai yawan mutane Biliyan uku.

Rahoton ya nanata cewa ganin yawan al’ummar duniya ya doshi biliyan tara nan da shekara ta 2040, daga Biliyan bakwai a yanzu, akwai bukatar yin wani abu cikin gaggawa.

Rahoton na cewa zuwa karshen shekara ta 2030, ana bukatar Karin abinci da kashi 50%, a bangaren wuta ko makamashi ana bukatar kashi 45% yayin da lamarin ruwa duniya na bukatar Karin kashi 30%.

Rahoton na cewa matakan da ake dauka yanzu wajen tunkarar matsalolin bassu gamsarwa, domin ana bukatar matakai ne masu karfi sosai, ta fannin tayar da komadan tattalin arzikin duniya.

A cewar rahoton duk da cewa yawan masu fama da matsanancin talauci ya ragu zuwa kashi 27% na duniya, idan aka kwatanta da shekara ta 2000, filayen noma masu yawa ake rasawa duk shekara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.