Isa ga babban shafi
MDD

Za’a samu hauhawan Farashin abinci a bana, inji MDD

Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya tace matsalar hauhawan farashin kayan abinci, da ke haifar da rigingimu a wasu kasashen Gabas ta Tsakiya da Nahiyar Afrika, zai ci gaba da tsawwala a shekarar 2012. 

Wasu manoma mata a kasar Habasha
Wasu manoma mata a kasar Habasha Mike Goldwater/Getty Images
Talla

Shugaban hukumar Abinci da aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya Jose Graziano da Silva wanda yake ganawa da manema labarai karo na farko, yace sabuwar shekarar da aka shiga, farashin kayan abinci zai kasance yadda yake.

Shugaban yace boren karancin cimaka da talauci da suka haddasa a wasu kasashen gabas ta tsakiya da kasashen Africa a shekarar 2011 za’a ci gaba da boren a shekarar 2012.

Sabon Shugaban yace zai yi kokari domin ganin cewa a zamaninsa an fita daga matsalar abinci.

Yace hukumar zata kai ziyara kasashe, domin ganin an kara himma sosai wajen ayyukan da aka dora mata, amma yace zai fifita Nahiyar Africa.

Sabon Shugaban Hukumar Farfesa Jose Graziano da Silva, mai shekaru 61 ya kasance na farko da ya hau kujerar Shugabancin hukumar daga yankin Latin Amurka,

Tun watan Yuni ne a bara aka nada shi don maye gulbin Jacque Diof wanda ya kwashe shekaru 17 yana shugabancin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.