Isa ga babban shafi

Dalilin da ya sa ECOWAS ke bukatar rundunar sojoji ta musamman -Amb Sani

An yi ganawa ta musamman a yau Talata tsakanin shugaban Najeriya da ke rike da mukamin shugaban kungiyar Afirka ta Yamma Ecowas/Cedeao Bola Ahmad Tinubu da takwarorinsa na kasashen Benin, da Guinea Bissau da kuma jamhuriyar Nijar, inda suka jaddada aniyarsu ta ganin cewa Dimokuradiyya ta dore a cikin kasashen yankin.

Shugabannin ECOWAS yayin taron da ya gudana a Abuja
Shugabannin ECOWAS yayin taron da ya gudana a Abuja © ECOWAS
Talla

Bayan ganawar ta su, an tattauna da jakadan Najeriya a ECOWAS Musa Nuhu Sani, ga kuma jawabin na sa.

"Abun da ya faru a makon jiya a kasar Guinea Bissau shi ne, shugabannin kasashen da ke karkashin ECOWAS sun gudanar taro, inda suka tattauna batutuwa da dama, ciki kuwa har da shirin Majalisar Dinkin Duniya na janye sojojinta daga Mali. Wannan kuma ya biyo bayan cimma matsayar haka a lokacin taron Majalisar tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin Mali suka mikawa bukatar hakan. A lokacin taron shugabannin ECOWAS sun cimma matsayar cewa za su dauki matakan da suka kamata kafin janye sojojin Majalisar Dinkin Duniya, don kar a sami wani gibin tsaro. Akan haka ne kungiyar ta yanke hukuncin cewa sabon shugaban kungiyar ta ECOWAS Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin Guinea Bissau Umarou Sisiko Mbalo da kuma na Jamhuriyar Benin Patrice Talon don yin bitar matakan da ya kamata ECOWAS ta dauka a lokacin taronta na gaba. Wannan dai wani mataki na toshe gibin da janye sojojin Majalisar Dinkin Duniya dubu 12 daga Mali zai haifar. Abinda ake gani dai shi ne, duk da kasan cewar sojojin na ci gaba aiki, ana samun kalubalen tsaro, don haka janyesu ba tare da an maye gurbinsu ba abun kara munana zayyi. Don haka an gudanar da taron na yau ne bisa abinda aka tattauna a makon jiya a Guine Bissau."

Kana ganin ECOWAS za ta iya samar da tsaron da ake bukata a Mali inda mutane ke ganin sojojin Faransa da kuma na Majalisar Dinkin Duniya sun gaza?

"Abinda muke cewa shi ne, ba zai yu wu shugabanni su nade hannunsu ba kawai duk da waccan fahimtar da wasu mutane ke da ita, domin a sha’anin tsaro a duk lokacin da makwabciyar ka ke da matsala, dole ne kaima ka shirya. Bugu da kari, wannan ba shi ne karo na farko da ECOWAS ke yin wani abu akan irin hakan ba, idan zaka iya tunawa akwai ECOMOG. Lokacin da aka samar da ECOMOG ba a kirkiri NATO ba. Lokacin ne ECOWAS ta tura da sojoji kasashen Liberia da kuma Sayo. ECOWAS ce kungiyar farko ta wata shiya a duniya da ta fara tura sojojinta wasu kasashe ba NATO ba. ECOWAS na da kwarewa. Tana da tsarinta na shiya wajen yaki da ta’addanci, wanda take son yin amfani da shi a yanzu. Haka nan akwai batun sojojin ko ta kwana na ECOWAS wanda suke kama da na ECOMOG da aka yi amfani da su a baya. Wannan ne abubuwan da shugabannin ke nazarin yadda za su yi amfani da su."

"(gama da dakatarwar da aka yiwa wasu kasashe daga ECOWAS) ba su bayyana dage dakatarwar ba, don sa ke maidosu cikin ECOWAS, amma suna cewar za a samar da wata kafa ta tattaunawa da shugabannin. Wannan ne dalilin da ya sa aka nada shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon don tattaunawa da su a matsayin jakadan Tinubu."

Kana nufin cewa kasashen Afrika za su iya kare Kansu ba tare da gudunmuwar wasu kasashe ba?

"Kwarai kuwa, za mu iya kare kanmu. Ko a nan Najeriya, muna yakar Boko Haram a shiyar Arewa maso Gabas shekaru 12 ke nan ba tare da gudunmuwar wasu kasashe ba. Abinda suke cewa shi ne tunda muna da wannan tsarin a kasa, abunda kawai ake bukata shi ne yadda za a samu kudin gudanar da shi daga cikin gida kafin fita waje. Amma in muka samu daga wajen muna bukata."

Samun dala biliyan biyu da miliyan dari biyar na da yawa. Za ku samu kuwa?

"Tsarin da muke da shi a kasa da na ke gaya maka, an amince da shi shekaru uku kafin annobar COVID, kuma abinda ake son tarawa shi ne dala biyan biyu da miliyan dari 3. A lokacin kasashen UEMOA da ke amfani da kudin CFA, su kimanin 8 sun yi alkawarin tara dala miliyan dari 5, Najeriya ta yi alkawarin bada dala miliyan dari 350 sai kuma Ghana da ta yi alkawarin dala miliyan 50 inda yakai julummar dala miliyan dari 9. Abinda ake so shi ne samun rabin abinde ake bukata, don fara aiki. Ko a jarabawa idan aka ci kashi 90 cikin 100 an yi nasara."

Ke nan kudi ba matsala ba ne?

"Haka ne wannan shine kudirinmu da yardar Allah."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.