Isa ga babban shafi

Tinubu ya zama sabon shugaban kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS

Shugabannin kasashen Yammacin Afirka da suka gudanar da taro yau lahadi a birnin Bissau, sun zabi takwaransu na Najeriya Bola Ahmed Tinubu a matsayin sabon shugaban kungiyar domin jagoranci na tsawon shekara guda, bayan da Umaru Cisseko Embalo na Guinea-Bissau ya kawo karshen wa’adin shugabancin kungiyar kasashen yankin wato ECOWAS.  

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu via REUTERS - POOL
Talla

Taron na ECOWAS a wannan karon da ke matsayin karo na 63 shi ne karon farko da shugaba Tinubu na Najeriya ke halarta a matsayin shugaban kasa.

Wasudagacikinmuhimmanbatutuwan da taronyatattauna sun hadajadawalinzabubbuka a kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea Conkary, tare da yinnazaridangane da yiyuwarkafawatarunduna ta musamman da za ta yaki ta’addanci da kumahanajuyinmulki a yankin. 

A jawabinsa na farko bayan karbar muhimman bayanai game da shugabancin kungiyar daga shugaba mai barin gado Umaro Embalo, Tinubu ya sha alwashin tabbatar da dorewar mulkin demokradiyya a kasashen yankin.

A cewar sabon shugaban na ECOWAS ya na daga cikin abubuwan da mulkinsa zai bai wa muhimmanci shi ne tabbatar da tafiyar da mulki karkashin demokradiyya da zaman lafiyar kasashe, yana mai cewa wannan batu ne da bazasu dauke shi da was aba.

Idan za a iya tunawa ko tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rike wannan mukami na shugabancin ECOWAS daga shekarar 2018 zuwa 2019, lura da yadda ake karba-karba tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

Kadan daga cikin nauyin da ke kan duk wani shugaban kungiyar ta ECOWAS shi ne tabbatar da sasanta duk wani rikici da ya taso tsakanin mambobin kungiyar ta hanyar hada kai da shugaban hukumar gudanarwar kungiyar baya ga tabbatar da bin dokoki da tanade tanaden kungiyar tsakanin mambobinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.