Isa ga babban shafi

Kotun ECOWAS ta koka da yadda kasashe basa mutunta hukuncinta

Shugaban kotun kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, mai sharia Edward Amoako Asante ya nuna takaicin sa kan yadda kasashe mambobin kungiyar ba sa aiwatar da hukuncin da kotun ta yanke.

Babban Ofishin kungiyar ECOWAS
Babban Ofishin kungiyar ECOWAS © wikipedia
Talla

A lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wajen bude sabon ofishin su a garin Abuja da ke tarayyar Najeriya, Asante ya ce kaso 30 ne kadai na hukuncin da suka yanke ake aiwatar. 

Ya ce kotun na taka muhimmiyar rawa wajen abinda ya shafi samar da zaman lafiya da gwamnati ta gari da kuma gudanar da komai a faifai a yankin. 

Asante ya kuma tabbatar da cewar za su ci gaba da bada tasu gudunmuwar da ta kamata ganin yadda kotun ke zama babban tubali a kungiyar ta ECOWAS.  

Shima shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta ECOWAS, Dr Alieu Touray ya nuna rashin jin dadin sa da yadda kasashe mambobin kungiyar basa aiwatar da hukuncin kotun, don haka ya bukaci su da su yi watsi da waccan dabi’a. 

Ya kuma bada tabbacin cewa samar da sabon ofishin zai samarwa kotun dukkanin abinda ta ke bukata wajen gudanar da aikin ta. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.