Isa ga babban shafi

Tawagar ECOWAS ta isa kasar Mali domin sasanta rikicin diflomasiyya

Wata babbar tawaga daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta isa kasar Mali domin kokarin warware rikicin diflomasiyya bayan da Bamako ta tsare sojojin Ivory Coast.

Shugabannin kasashen ECOWAS a birnin Accra. 25 ga Maris, 2022.
Shugabannin kasashen ECOWAS a birnin Accra. 25 ga Maris, 2022. AP - Misper Apawu
Talla

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow da takwaransa na Ghana Nana Akufo-Addo sun sauka a filin jirgin saman Bamako inda suka nufi ofishin shugaban kasar ta Mali.

Ana sa ran shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe zai shiga tawagar amma a maimakon haka ya samu wakilcin ministan harkokin wajen kasar Robert Dussey wanda ya tabbatar da kasancewarsa a babban birnin kasar Bamako.

Mali da Ivory Coast na takun sakar diflomasiyya kan makomar sojojin Ivory Coast su 46 da aka kama a ranar 10 ga watan Yuli a lokacin da suka isa filin jirgin saman kasar.

Ivory Coast da Majalisar Dinkin Duniya sun ce ya kamata sojojin su taimaka wajen samar da tsaro ga tawagar kasar Jamus dake aikin wanzar da zaman lafiya a Mali, sai dai Bamako ta zarge su da kasancewa sojojin haya, da suka zo yi wa harkokin tsaro zagon kasa.

Gwamnatin mulkin sojan Mali da ke kan karagar mulki tun shekarar 2020 ta yi gargadin cewa za ta saurari masu shiga tsakani na ECOWAS amma ba za ta karbi umarninsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.