Isa ga babban shafi

Tinubu zai halarci taron ECOWAS karon farko a matsayin shugaban kasa

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai tafi kasar Guinea-Bissau domin halartar taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS karo na 63.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu via REUTERS - POOL
Talla

Shugaban dai zai samu rakiyar wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun sa, Dele Alake ta bayyana.

Taron da za a za a fara a gobe Lahadi, ana sa ran za a tattauna batutuwan da suka shafi yankin yammacin Afrika, musammanma rahoton zaman taro na 50 na kwamitin samar da zaman lafiya na kungiyar wanda ya kunshi kalubalen tsaro da kasashe mambobin kungiyar ke fuskanta.

Haka nan akwai rahoton zaman taro na 90 na majalisar ministocin kungiyar ta ECOWAS kan harkokin kudi da aiwatar da kawusanci na bai daya a nahiyar Afirka da kuma rahoto kan halin da ake ciki a Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.

Sauran abubuwan da aka saran tattaunawa a yayin taron, sun hada da shirin ECOWAS na samar da kudin bai daya da da dai sauran su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.