Isa ga babban shafi

Tawagar ECOWAS na ziyara a Burkina Faso kan tsaro

Yanzu haka wata tawagar jami’an kungiyar Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS na ci gaba da ziyarar aiki a Burkina Faso, domin samun cikakkun bayanai dangane da bukatun al’ummomin da ke rayuwa a yankunan da ke fama da matsalar tsaro da ta addabi kasar.

Wakilan Kungiyar ECOWAS na ziyara kan yadda za'a taimakawa kasar da ke fama da matsalar rashin tsaro.
Wakilan Kungiyar ECOWAS na ziyara kan yadda za'a taimakawa kasar da ke fama da matsalar rashin tsaro. AFP - NIPAH DENNIS
Talla

Tawagar, wadda ta isa Burkina Faso tun ranar 21 ga wannan wata na Maris, za ta yi kokarin tantance adadin mutanen da ke bukatar taimako ne, duk da cewa tuni Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa akwai mutane akalla miliyan daya da dubu dari 900 da suka kaurace wa muhallansu sakamakon tashe-tashen hankula.

Dr Ugbe Sintiki, daraka a sashin kula da ayyukan jinkai a kungiyar ta ECOWAS/CEDEAOd, a zantawarta da manema labarai a birnin Ouagadougou bayan sun zagaya wasu yankuna na kasar, ta bayyana halin da al’umma ke ciki da cewa yana matukar tayar da hankula.

Dr Ugbe, ta ce mafi yawan mutane na fama da matsalar yunwa da matsalar karancin ruwan sha da rashin samun kula a fannin kiwon lafiya da kuma muhalli. To amma duk da haka, jami’ar ta ECOWAS ta jinjina wa gwamnatin Burkina Faso da sauran kungiyoyi na agaji, a game da kokarin da suke domin tallafa wa mata da yara kanana da ke rayuwa a matsugunai na wucin gadi.

Bayan wannan ziyara, tawagar za ta gabatar wa Hukumar Gudanarwa ta Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka ECOWAS da kuma gwamnatin Burkina Faso cikakken rahoto, wanda zai fayyace bukatun al’ummar da ke fama da matsaloli sakamakon yakin da kasar ke fama da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.