Isa ga babban shafi

Mali ta gindaya sharudda gabanin ziyarar da ECOWAS za ta kai kasar

Gwamnatin Sojin Mali ta gindaya sharudda gabanin ziyarar da jagororin kungiyar ECOWAS za su kai kasar dangane da bukatar sakin Sojin Ivory Coast 46 wadanda Bamako ke rike da su fiye da watanni 2.

Shugaban gwamnatin Sojin Mali kanal Assimi Goita.
Shugaban gwamnatin Sojin Mali kanal Assimi Goita. AFP - NIPAH DENNIS
Talla

Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop ya yi gargadin cewa, kasar sa bazata lamunci matakan da shugabannin kungiyar ECOWAS ke shirin dauka a ziyarar da za su kai kasar cikin makon nan a kokarin sasanta rikicin diflomasiyyar da ke tsakaninta da makwabciyarta Ivory Coast.

A wata zantawarsa da manema labarai a birnin Bambara Diop ya bayyana cewa za su saurari abin da shugabannin za su fada, amma dole ya kasance anbi matakan da suka gindaya

Yayin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da ya gudana cikin makon jiya a New York ne, kungiyar ta ECOWAS ta cimma matsayar aikewa da jakadu na musamman Mali da suka kunshi shugabannin kasashen Ghana da Senegal da kuma Togo don shiga tsakani a rikicin da ke gudana tsakaninta da makwabciyarta Ivory Coast, tawagar da ake sa ran ta isa kasar tsakanin gobe Alhamis ko kuma jibi Juma’a.

Sai dai Abdoulaye Diop ya bayyana cewa, wajibi shiga tsakanin na ECOWAS ya yid ai dai da bukatar bangaren shari’ar kasar dangane da sharuddan da ta gindaya gabanin sakin sojojin na Ivory Coast 46.

Tun a ranar 10 ga watan Yulin da ya gabata ne Mali ta kame Sojin Ivory Coast 49 jim kadan bayan saukarsu a filin jirgin saman Bamako gabanin sakin matan cikinsu 3 a baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.